22 Afirilu 2020 - 05:29
WHO: Mun Sanar Da Duniya Bayanai Game Da COVID-19 Tun Farkon Bullarta

Hukumar lafiya ta duniya WHO a takaice, ta bayyana cewa, ta yi aiki kafada da kafada da masana daga kasar Amurka, musamman bayan barkewar COVID-19, kuma tun lokacin da cutar ta barke, ba ta boye komai game da cutar ga sauran kasashe ba.

(ABNA24.com) Hukumar lafiya ta duniya WHO a takaice, ta bayyana cewa, ta yi aiki kafada da kafada da masana daga kasar Amurka, musamman bayan barkewar COVID-19, kuma tun lokacin da cutar ta barke, ba ta boye komai game da cutar ga sauran kasashe ba.

Babban darektan hukumar Tedros Adhanom Ghebreyesus, shi ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi a taron da hukumar ta shiya ta kafar bidiyo daga Geneva.

Ya ce, hukumarsa da cibiyar hana yaduwar cututtuka ta Amurka (CDC), sun dade suna hadin gwiwa, kuma babu wani abin da aka boyewa hukumar game da wannan annoba.

Mista Ghebreyesus, ya ce, "Mun yi ta yin gargadi, mun yi ta yin gargadi tun lokacin da aka samu rahoton bullar cutar. Wannan abokiyar gaba ce da kowa zai yaka, muna bukatar hadin kai, da sadaukar da kai daga kasashen duniya don ganin bayan wannan annoba.

Bayannin na WHO, na zuwa ne ‘yan kwanaki kadan bayan zargin da shugaba Donald Trump na Amurka ya yi cewa, WHO ta boye bayanai game da barkewar cutar, alhali bayanai daga Amurkar sun ce, manyan jami'an lafiya na kasar sun yi ta ganawa akai-akai da takwarorinsu na WHO.


/129